Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu a Gaza ta sanar a ranar Talata cewa adadin Falasdinawa da aka kashe a Gaza a rana ta 347 da ake ci gaba da gwabza yakin kisan kare dangi na Isra’ila ya kai 41,252 tare da jikkata mutane 95,497.
A cikin rahotonta na yau da kullun, ma’aikatar ta ambaci cewa sojojin mamaya na Isra’ila sun yi kisan kiyashi uku a Gaza, inda suka kashe mutane 26 tare da raunata wasu 84 a cikin sa’o’i 24 kacal, ba tare da kirga wadanda aka kashe a sabon kisan gilla ba.
Dakarun mamaya na Isra’ila sun yi wani kisan kiyashi a ranar Talatar da ta gabata a sansanin ‘yan gudun hijira na al-Bureij da ke tsakiyar Gaza, inda suka auna wani yanki mai yawan jama’a, inda suka kashe sama da mutane 50, kamar yadda wakilin Al Mayadeen ya tabbatar.
Hukumar kare fararen hula a Gaza ta bayar da rahoton cewa, an harba bama-bamai a yankin da ake ciki ta hanyar amfani da manyan bama-bamai da Amurka ta kera.
An yi nuni da cewa, jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun bude wuta kan jami’an tsaron fararen hula a lokacin da suke isa wurin da aka yi kisan kiyashi, lamarin da ya kawo cikas ga kokarin ceto wadanda suka jikkata da kuma kwashe gawarwakin shahidan.