Search
Close this search box.

Gaza : Adadin Wadanda Suka Mutu Sakamakon Hare-haren Isra’ila Ya Kai 35,233

Adadin wadanda suka mutu sakamakon hare-haren da Isra’ila ta ke ci gaba da kaiwa a zirin Gaza ya kai 35,233, in ji ma’aikatar lafiya ta

Adadin wadanda suka mutu sakamakon hare-haren da Isra’ila ta ke ci gaba da kaiwa a zirin Gaza ya kai 35,233, in ji ma’aikatar lafiya ta yankin a ranar Laraba.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ta ce akalla wasu mutane 79,141 ne kuma suka jikkata tun soma farmakin.

Ma’aikatar ta ce “Sojojin Isra’ila sun kashe mutane 60 tare da jikkata wasu 80 a wani hari da aka kai wa wani gida a cikin sa’o’i 24 da suka gabata.”

Da yawan wadanda abin ya shafa na makale a karkashin baraguzan gine-gine da kuma kan tituna, inda masu ceto suka kasa kai musu dauki.

Isra’ila dai na kai hare-hare ba kakkautawa a Zirin Gaza tun bayan harin ba zata na Hamas a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya yi sanadin mutuwar ‘yan Isra’ila kusan 1,200.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments