Search
Close this search box.

Ganawar Manyan Kwamandojin Sojin Ruwan Kasashen Iran Da Na Afrika Ta Kudu

Manyan kwamandojin sojin ruwan kasashen Iran da Afrika ta Kudu, sun gana a birnin Tehran, da nufin karfafa fannoni da dama a tsakaninsu. Admiral Monde

Manyan kwamandojin sojin ruwan kasashen Iran da Afrika ta Kudu, sun gana a birnin Tehran, da nufin karfafa fannoni da dama a tsakaninsu.

Admiral Monde Lobse, kwamandan rundunar sojojin ruwan kasar Afirka ta Kudu tare da tawagarsa, ya gana da takwaransa, Admiral Shahram Irani a hedikwatar sojojin ruwan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

A cewar rahoton hulda da jama’a na rundunar, kwamandan sojojin ruwa na Afirka ta Kudu ya kuma ziyarci rundunar sojojin ruwa ta kudancin kasar Iran da jami’ar Nowshahr da wsu wurare na karin ilimi na sojojin ruwa.

Bangarorin sun bayyana fatansu na cewa nan gaba kadan, za su iya kara karfin aiki da kayan aiki da karfafa sashen fasaha na rundunar sojojin ruwa, da tura dalibai zuwa kasashen biyu don karin hadin kai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments