Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya nakalto ganawar da aka yi a tsakanin mataimakan ministocin harkokin waje na kasashen Saudiyya, Walid Khariji, da na China Miao Deo da kuma ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci.
A yayin wannan taron, ministan harkokin wajen Iran ya bayyana gamsuwarsa da yadda kasar China take daukar matakai na gina kyakkyawar alaka a cikin yannacin Asiya, sannan kuma ya bayyana matsayar Iran na bunkasa alakarta da kasashe makwabta.
Ministan harkokin wajen na Iran ya yi Ishara da yadda alaka a tsakanin Tehran da Riaydh take bunkasa a cikin fagage mabanbanta, haka nan kuma yadda suke tuntubar juna akan batutuwan da kasashen biyu suke bai wa muhimmanci.
Haka nan kuma ya yi Ishara da rawar da kasar china ta taka wajen karfafa zaman lafiya a tsakanin kasashen Iran da Saudiyya, da kuma taimakawa a wajen aiki da doka a duniya.
Minista Arakci ya kuma tabo batun alaka a tsakanin Iran da China yana mai kara da cewa, kasashen biyu sun daura aniya fadada wannan alakar.
A nasu gefen, jami’an diplomasiyyar na Saudiyya da China sun yaba wa Iran akan yadda ta karbi bakuncin taron kasashen uku wanda shi ne karo na uku. Haka nan kuma sun nuna azamarsu ta ganin an fadada wannan alakar.
Gabanin wannan ganawar, jami’an diplomasiyyar na China da Saudiyya sun gana da takwaransu na Iran Majid Takht-Ravanchi akan batun karfafa alakar kasashen uku.
Sanarwar ta sake jaddada kudirin Iran da Saudiyya na bin dukkan tanade-tanaden Yarjejeniyar Beijing ta 2023, wanda ya sauwaka wajen dawo da huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu a shiga tsakani na China.