Wakiliyar musamman ta MDD akan Falasdinu Francesca Albanze ta sanar da cewa; Bayanan da jaridar ” New York Times” ta buga masu kunshe da hotuna na laifin kashe masu aikin ceto a Rafah, suna dakile riwayar Isra’ila.”
Wakiliyar ta MDD ta fada wa tashar talabijin din Aljazeera cewa, abinda ya faru kisan kiyashi ne’ sannan ta kara da cewa sojojin Isra’ilan suna yin abinda suke yi ne a tsare,kuma duniya ta yi shiru.”
Jaridar “New York Times” ta watsa faifen bidiyo dake dauke da muryar wani ma’aikacin agaji wanda daya ne daga cikin wadanda aka sami gawawwakinsu a cikin wani babban kabari a yankin Rafah. Bidiyon ya nuna yadda sojojin Isra’ila su ka kai wa masu aikin agaji hari da gangan, sun kuma san cewa su ne saboda alamomin da suke tattare da su.
Riwayar da HKI ta watsa ita ce, cewa motocin masu aikin agajin sun nufi inda sojojinsu suke ne gadan-gadan cikin shakku.”
Wakiliyar MDD ta kuma kara da cewa; wannan laifin da HKI ta tafka bai kamata a kalle shi nesa da sauran laifukan da take aikatawa ba a Gaza, tana mai kara da cewa; Tun 2023 take yi wa al’ummar Gaza kisan kiyashi a tsare.