Fiye Da Mata 300 Ne Cikinsu Ya Zube Saboda  Rashin Abinci Mai Gina Jiki A Gaza

Ofishin watsa labaru na hukuma a Gaza ya yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da kuma kungiyoyin jin kai, da su yi aiki da

Ofishin watsa labaru na hukuma a Gaza ya yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da kuma kungiyoyin jin kai, da su yi aiki da nauyin da ya rataya a wuyansu na doka da kyawawan halaye, su tsoma baki domin ceto da fararen hula a Gaza.

Ofishin watsa labarun na hukuma a Gaza ya  kuma yi kira da a tseratar da mutanen na Gaza daga yunuwar da suke fuskanta, ta hanyar yin matsin lamba da a bude hanyoyin shigar da kayan taimako da agaji cikin yankin.

Ita kuwa hukumar lafiya ta yanki ta sanar da yadda sojojin na HKI suke ci gaba da kai hare-hare akan  asibitoci da sauran cibiyoyin kiwon lafiya da hakan ya sabawa dokokin yaki.

Ofishin watsa labaru na hukumar Gaza ya kuma sanar da cewa; Har yanzu yankin yana fama da matsanancin killace shi da aka yi, da hana shigar da kayan agaji.

Daga lokacin sake komawa yaki na bayan nan da HKI ta yi, tun kwanaki 80 da su ka gabata,mutane 58 sun rasa rayukansu saboda rashin abinci mai gina jiki, sai kuma wasu 242 da yunuwa da rashin magani su ka kashe,mafi yawancinsu wadanda su ka mayanta.  Haka nan kuma wasu mata masu ciki fiye da 300 su ke cikin nasu ya zube saboda rashin abinci mai gina jiki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments