Fiye Da Falasdinawa 900,000 Ne Su Ka Yi Hijira A Cikin Gaza

 HKI tana ci gaba da kai wa muhimman cibiyoyi da gidajen Falasdinawa a fadin Gaza. Majiyar Falasdinawa ta ce daga safiyar yau Laraba adadin wadanda

 HKI tana ci gaba da kai wa muhimman cibiyoyi da gidajen Falasdinawa a fadin Gaza.

Majiyar Falasdinawa ta ce daga safiyar yau Laraba adadin wadanda su ka yi shahadar sun kai 45 sanadiyyar hare-haren da jiragen yakin ‘yan sahayoniyar su ka kai.

Har ila yau an sami wasu Karin shahidan biyar a wuraren karbar agaji dake arewacin Rafaha.

A wani labarin mai alaka da hakan shugaban hukumar lafiya ta duniya        ( w.h.o) Tedross Adhanom ya ce; Kai hare-haren da ake yi a kusa da asibitin Rantisy, dake Gaza, ya yi sanadiyyar tsayuwar aikin Asibiti, domin rashin tsaro.

Har ila yau ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta kara da cewa; Jinkirin shigar da makamashi zuwa yankin yana barazanar tsayar da aikin injinan da suke bayar da wuta a asibitin idanu,wanda yake yi wa mutane da dama aiki.

Ofishin hukuma a Gaza ya sanar da cewa, mutanen da sun kai 900,000 sun fice daga gidajensu amma kuma suna ci gaba da riko da ci gaba da zamansu a cikin kasarsu.

Bugu da kari, ‘yan mamayar suna ci gaba da tilastawa mutanen na Gaza ficewa daga gidajensu, zuwa yankunan kudancin Gaza, ta hanyar kai musu hare-hare.

Haka nan kuma da akwai wasu Karin mutanen 334,000 da aka fitarsa fita daga gidajensu a cikin kwanaki uku, da hakan ya sa yawansu ya kai 60,000.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments