Fiye Da Falasdinawa 300 Ne Su Ka Yi Shahada Da Jikkata Daga Safiyar Yau Juma’a

HKI tana ci gaba da yi wa Falasdinawa kisan kiyashi a  Gaza wanda ya ci rayukan Falasdiniwa  kusan 300 da su ka hada kananan yara

HKI tana ci gaba da yi wa Falasdinawa kisan kiyashi a  Gaza wanda ya ci rayukan Falasdiniwa  kusan 300 da su ka hada kananan yara da mata.

Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta ambaci cewa;Tun da asubahin yau ne dai sojojin mamayar su ka fara kai wadannan munanan hare-haren wanda ba komai ba ne, sai kisan kiyashi akan Falasdinawada suke fama da matsananciyar yunwa saboda rashin abinci.

Bugu da kari, mafi yawancin Falasdinawan da HKI take kai wa hare-haren suna rayuwa ne a cikin hemomi bayan da ta rushe musu gidajensu.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinu ta sanar a cewa; A cikin sa’oi 24 da su ka gabata, adadin wadanda su ka yi shahada sun kai 109, kuma tuni an fito da gawawwakinsu daga gine-gine da hemomin da su ka fada a kansu, yayin da wasu 216 su ka jikkata.

A jiya kadai, adadin Falasdinawan da su ka yi shahada sun haura 100. Baya ga wadanda su ka yi shahadar, da akwai kuma wani adadi na falasdinawa da ya kai 100 da sun bace.

Daga 7 ga watan Oktoba na 2023 zuwa yanzu, adadin Falasdinawan da su ka yi shahada sun kai dubu 53, da 119, sai kuma wadanda su ka jikkata da sun kai 120,114.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted