Fira ministan Indiya ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana kokari da zage dantse wajen taimakawa a fagen inganta zaman lafiyar yanki da na duniya baki daya
Fira ministan Indiya Narendra Modi ya yaba da rawar da Iran ta taka wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya, yana mai cewa: Gwamnatin Indiya tana goyon bayan kokarin Iran na karfafa zaman lafiya a yankin da ma duniya baki daya, yana mai jaddada bukatar warware takaddama ta hanyar diflomasiyya, ciki har da na Iran da Amurka.
Har ila yau fira ministan na Indiya ya bayyana matukar bakin cikinsa dangane da abin da ya faru a tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’e da ke lardin Hormozgan a kudancin kasar Iran, ya kuma bayyana cewa kasarsa a shirye take ta ba da duk wani taimako ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Modi ya bayyana kyakkyawar fatansa na lafiya da burinsa ga shugaban kasar Iran da jagoran juyin juya halin Musulunci da kuma ci gaba da wadata ga al’ummar Iran masu girma.