Farfesa Jibril Amin Likita kuma tsohon malamin Jami’a, ya rasu a jiya Laraba yana dan shekara 85 a duniya.
Jaridar Daily Trusta ta Najeriya ta nakalto majiyar iyalar mamacin na tabbatar da haka. Ta kuma bayyana cewa kwamishin gidaje a jihar Adama Hon Abdullahi Prambe ya tabbatar da labarin. Sannan ya kara da cewa an yi masa sallar Jana’iza a babban masallacin kasa a Abuja a yau Alhamis. Sannan za’a maida shi garinsa Song na jihar Adamawa inda za’a rufe shi.
A rayuwarsa dai Farfesa AAmin likitan zuciya ne, sannan malami da shugaba Jami’ar Maiduri na Jahar bornin a wani lokaci, ya kuma karantar. Har’ila yau Farfesa Amin ya rike kujerar Ministan ilmi da manfetur, sannan jakadan Najeriya A Amurka sannan yan majalisar dattawa mai wakiltan Adama ta tsakiya.