Fararen Fatar Kasar Afirka Ta Kudu Sun Yi  Gangamin  Nuna  Goyon Bayan Trump

A jiya Asabar ne da wasu kungiyoyi na fararen fata a kasar Afirka ta kudu sun yi  gangami a bakin ofishin jakadancin Amurka dake birnin

A jiya Asabar ne da wasu kungiyoyi na fararen fata a kasar Afirka ta kudu sun yi  gangami a bakin ofishin jakadancin Amurka dake birnin Pretoria suna masu nuna goyon bayansu ga kalaman da Donald Trump  da ya riya cewa, gwamnatin kasar da bakaken fata masu rinjaye tana nunawa fararen fata wariya.

Daruruwan masu gangamin sun daga kwalaye da aka yi rubuta a jikinsu da su ka kunshi yin godiya ga Donald Trump da ya yi Magana akan abinda ce, damuwarsu ce.

Wanda ya  shirya gangamin Willem Petzer, ya  ce, yana son fadawa kasashen turai cewa,  suna da kawaye a cikin kasar Afirka ta kudu.

Da dama daga cikin mahalarta gangamin sun fito ne daga al’ummar Afirkana da Trump ya ce, gwamnatin kasar ta yi dokar kwace musu filaye.

Shi kuwa Heinrich Steinhausen ya bayyana cewa; A cikin shekaru 30 na bayan nan an sami rabuwar kawuna a cikin kasar saboda abinda ya kira siyasar gwamnati.

Tuni dai gwamantin kasar Afirka ta kudu ta yi watsi da wadannan zarge-zargen na Donald Trump.

Masu bin diddigin abinda yake faruwa suna ganin cewa Amurkan tana yin matsin lamba ne akan kasar Afirka ta kudu saboda ta shigar da kasar “Isra’ila” a gaban kotun duniya ta manyan laifuka da ta yanke hukunci akan Isra’ila da yi wa Falasdinawa kisan kiyashi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments