Faransa ta jaddada aniyarta na ci gaba da tattaunawar nukiliyar iran

Kasar faransa ta jaddada anniyar na ci gaba da tattaunawa kan shirin nukiliyar iran. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Faransa ya bayyana a ranar Alhamis cewa,

Kasar faransa ta jaddada anniyar na ci gaba da tattaunawa kan shirin nukiliyar iran.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Faransa ya bayyana a ranar Alhamis cewa, Faransa na ci gaba da jajircewa wajen ganin an warware matsalar nukiliyar Iran ta hanyar diflomasiyya, kuma a shirye take ta ci gaba da tattaunawa da Tehran.

A yayin taron manema labarai na mako-mako a birnin Paris, Christophe Lemoine ya jaddada cewa: “Muna ci gaba da jajircewa wajen warware matsalar nukiliyar Iran ta hanyar diflomasiyya, kuma a shirye muke mu ci gaba da tattaunawa da Tehran.”

Wannan bayanin na zuwa ne bayan da ministan harkokin wajen Iran Seyyed Abbas Araghchi ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na X cewa, Tehran a shirye ta ke ta ci gaba da tattaunawa da kasashen Turai, inda ya bayyana cewa tattaunawar za ta iya bude wata sabuwar hanya.

Araghchi ya bayyana cewa, bayan shawarwarin baya-bayan nan da aka yi a Moscow da Beijing, a shirye yake ya ziyarci Paris, Berlin da London.

Ya kuma ce tun kafin fara tattaunawar da Amurka, Iran na shirye, amma kasashen Turan uku da batun ya shafa ba su nuna sha’awarsu ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments