A Faransa daruruwan mutane ne suka-yi zanga-zanga a birnin Paris don nuna adawa da hirar da wani gidan talabijin din kasar ya yi da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, masu zanga-zangar sun gudanar da zanga-zangar lumana don nuna adawa da hirar da aka yi da firaministan Isra’ila a wajen ofishin gidan talabijin na Faransa mai zaman kansa, TF1, a yammacin birnin Paris.
Jami’an ‘yan sanda sun hana su shiga ginin.
Masu zanga-zangar rike da tutocin Falasdinu suna rera kallamai: “Gaza, Paris na tare da ku”, “A tsagaita bude wuta nan da nan!”, “Isra’ila, mai kisan kai”.
A cikin hirar da aka watsa a tashar labarai ta TF1 ta LCI, Netanyahu ya kare yakinsa a Gaza kuma ya shaida cewa “yawan asarar farar hula idan aka kwatanta da asarar mayakan [Falasdinawa] shine mafi karancin adadin da muka gani a yakin cikin birane”.
Netanyahu ya ci gaba da da’awar cewa Isra’ila ba ta kai hari kan fararen hula, ko kuma da gangan take kokarin haifar da yunwa ba.
Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin agaji da gwamnatocin kasashen ketare sun ce Gaza na fama da yunwa sakamakon takunkuman Isra’ila na hana shigar da agajin jin kai a yankin, inda aka kashe akalla Falasdinawa 36,224 tare da jikkata 81,777 tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.
Sama da mutane miliyan ne kuma suka rasa matsugunansu yayin da Isra’ila ke ci gaba da mamaye birnin Rafah duk da Allah wadai da umarnin kotun duniya da ke birnin Hague na ta janye daga birnin.