Falasdinawa Sun Gano Gawakin Wadanda HKI Ta Kashe A gaza  Fiye Da 320 Cikin Kwanaki Biyu Kacal

 Magu ayyukan ceto a gaza sun gano gawakin Falasdinawa fiye da 320 a karkashin burbushin gine-ginen da aka rusa. Tashar talabijin ta Presstv a nan

 Magu ayyukan ceto a gaza sun gano gawakin Falasdinawa fiye da 320 a karkashin burbushin gine-ginen da aka rusa.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa tun bayan fara yakin tufanul Aksa shekaru biyu da suka gabata Falasdinawa kimani fiye da 10,000 suka bace. Kuma a zatun mafi yawansu suna bisne a karkashin burbushi na gine-ginan da HKI ta rusa a kansu a zikin gaza.

Asbitoci a gaza ya zuwa yansu sun bada sanarwan karban gawakin Falasdinawa 323 wadanda aka zakulo karkashin burbushin gine-gine. Da HKI ta rusa a kansu.

Labarin ya kara da cewa a lissafin MDD ya zuwa tsagaita budewa juna wuta a gaza HKI ta rusa gidajen falasdinawa 430,000 a gaza.

Banda haka akwai wasu Falasdinawa kimani miliyon daya wadanda suke bukatar taimakonlikitoce kafin su koma hayyacinsu saboda abubuwan bantsaro da suka gani.

A wani labarin kuma an bada sanarwan cewa an fara shigo da kayakin abinci da magunguna a gaza a safiyar yau, kuma a kowace rana mutocin trela 600 zasu shiga Gaza da kofofin Rafa da kuma karim saleh.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted