Falasdinawa Sun Caccaki Jami’ar MDD Kan Rashin Ambaton Kisan Kare Dangi A Gaza

Falasdinawa sun caccaki jami’in Majalisar Dinkin Duniya kan rashin ambaton kisan kare dangi a Gaza. Wani jami’in Falasdinu ya zargi Alice Wairimu Nde-Ritu, mai ba

Falasdinawa sun caccaki jami’in Majalisar Dinkin Duniya kan rashin ambaton kisan kare dangi a Gaza.

Wani jami’in Falasdinu ya zargi Alice Wairimu Nde-Ritu, mai ba da shawara ta musamman kan hana kisan kiyashi ga Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da “kasa yin aiki da umarninta”.

A yayin jawabin da ta yi a ranar Talata a taron kwamitin sulhu kan kare fararen hula a rikicin da ake yi da makamai, Alice Wairimu Neritu ta yi magana sosai kan Sudan amma bata ambaci yakin da Isra’ila ke yi a Gaza ba.

“Akwai gazawa wajen bin umarninta ta hanyar yanke shawarar cewa ba za ta ce komai ba game da halin da Falasdinawa ke ciki a Gaza, yayin da a halin yanzu ICJ ke binciken zargin kisan kiyashin da ake yi wa Isra’ila,” in ji mataimakin jakadan Falasdinu a kotun ICJ, Majed Bamya.

Ba a yi magana kan Gaza ba yayin da ake magana kan rigakafin kisan kare dangi inji jami’in a daidai lokacin da Isra’ila ke raba falasdianwa da duk wani abu da ake bukata domin rayuwa.

Adadin dai falasdinawan da suka rasa rayukansu a Gaza, tun bayan harin ramuwar gayya na Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba ya kai 35,857.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments