Falasdinawa 8,000 Ne Suke Karkashin Baraguzan Gine-Gine

Majiyar Falasdinawa ta ce: Akwai gawawwaki 8,000 a ƙarƙashin baraguzan gine-gine, kuma ana jana’izar gawarwakin shahidai 75 a yankin na Gaza Ma’aikatar Lafiya ta Gaza

Majiyar Falasdinawa ta ce: Akwai gawawwaki 8,000 a ƙarƙashin baraguzan gine-gine, kuma ana jana’izar gawarwakin shahidai 75 a yankin na Gaza

Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta sanar da jana’izar gawarwakin shahidai 75 da aka samo daga ƙarƙashin baraguzan gine-gine da suka lalace a unguwar al-Daraj da ke birnin Gaza. A halin yanzu, majiyoyi a asibitocin Gaza sun ruwaito cewa an kashe Falasdinawa biyar, ciki har da yara biyu, yayin da wasu 11 suka jikkata sakamakon gobarar da sojojin mamayar Isra’ila suka kunna tun daga safiyar yau Lahadi.

Wakilin gidan talabijin na Al- Jazeera Nour Khaled ya ruwaito cewa: An gano gawarwakin shahidai kusan shekaru uku bayan harin bama-bamai da sojojin mamayar Isra’ila suka kai a yankunan gabashin birnin Gaza, musamman unguwannin al-Tuffah da al-Daraj. An lura cewa yawancin wadanda abin ya shafa yara ne da mata da ke cikin gidajensu lokacin da aka kai musu hare-haren.

Rahoton ya ƙara da cewa: ƙungiyoyin kare fararen hula ba su iya isa ga gawarwakin a lokacin ba, saboda sojojin mamayar Isra’ila sun hana shiga wuraren da aka gudanar da kashe-kashen gillar kan Falasdinawa, kafin daga baya a yi nasarar kutsawa cikin yankunan don gudanar da ayyukan da aka bayyana a matsayin masu wahala.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted