Falasdinawa 40 ne suka yi shahada a hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan Zirin Gaza tun daga wayewar garin jiya Juma’a
Rahotonni sun bayyana cewa: A yammacin jiya Juma’a, Falasdinawa fararen hula 8 ne suka yi shahada yayin da wasu kuma suka jikkata sakamakon wani hare-haren da jiragen saman sojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gida a sansanin Jabaliya da al-Balad da ke arewacin zirin Gaza.
Haka zalika hare-haren sun yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa 6 sannan wasu 8 suka jikkata a wani harin da jiragen saman yakin mamayar Isra’ila suka kai kan taron fararen hula da ke kusa da mahadar Abd al-Aal da ke kan titin al-Jala’a da ke arewacin birnin Gaza.
A cewar majiyoyin cikin gida, jiragen saman yakin mamayar Isra’ila sun kai hari kan wani asibiti da ke titin al-Jala’a, inda suka janyo shahadan Mahmoud Abdullah al-Muqayyad, Ahmed Qaza’ar, Tamer Hamdan, Samer al-Nuwairi, Hatem al-Sa’ati, da Rizq al-Madhoun.
A kudancin zirin Gaza kuwa, Falasdinawa uku ne suka yi shahada, kuma wasu suka jikkata, lokacin da wani jirgin saman yakin mamayar Isra’ila ya kai hari kan wata tanti da ke dauke da ‘yan gudun hijira a yankin Mawasi na Khan Yunis.
Sojojin mamayar Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza a rana ta 46 a jere, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane, da jikkatan wasu na daban