Falasdinawa 39 Ne Suka Yi Shahada Sakamakon Hare-Haren Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Falasdinawa 39 ne suka yi shahada wasu adadi mai yawa kuma suka jikkata a wasu hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai kan Gaza Rahotonni sun

Falasdinawa 39 ne suka yi shahada wasu adadi mai yawa kuma suka jikkata a wasu hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai kan Gaza

Rahotonni sun bayyana cewa; Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai munanan hare-hare kan yankunan Zirin Gaza, inda suka janyo shahadan Falasdinawa 39 tare da jikkatan wasu da dama, sakamakon hare-haren wuce gona da iri da suka fara kai wa tun daga wayewar garin Lahadi, mafi yawan wadanda harin ta ritsa da su ‘yan gudun hijira ne da suka samu mafaka a makarantar Khalil Aweida da ke Ezbat Beit Hanoun a arewacin Zirin Gaza, sannan sojojin mamayar sun gudanar da samame a yankunan daban-daban tare da kama matasa masu yawa.

Wakilin Aljazeera ya bayyana cewa: Sama da Falasdinawa 15 ne suka yi shahada a harin da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a makarantar Khalil Aweida da ke Ezbet Beit Hanoun a arewacin Zirin Gaza, kuma suka kama mutanen tare da tilastawa mata da yara barin makarantar da karfin bindiga.

A kudancin zirin Gaza kuwa, wakilin ya rawaito cewa: Wani Bafalasdine ya yi shahada a wani harin da wani jirgin sama maras matuki na haramtacciyar kasar Isra’ila ya kai kan Khirbet Al-Adas da ke arewacin birnin Rafah. Sannan an kuma wasu Falasdinawa biyu sun yi shahada a wani hari da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a unguwar Al-Amal da ke yammacin birnin Khan Yunis.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments