Falasdinawa 3 Sun yi Shahada Sakamakon Hare-Haren Isra’ila A Yankin Gaza A Jiya Laraba

Majiyoyin labarai sun bayyana cewa akalla falasdinawa guda 3 sun  yi shahada a jiya laraba bayan wasu hare-haren da sojojin isra’ila suka kai a arewaci

Majiyoyin labarai sun bayyana cewa akalla falasdinawa guda 3 sun  yi shahada a jiya laraba bayan wasu hare-haren da sojojin isra’ila suka kai a arewaci da kudancin yankin gaza. majiyar Asibiti a kudancin gaza a Asibitin Nasir busil sun ga gawar wani bafalasdine , kuma wasu guda 16 sun jikkata cikinsu har da yara kanana sakamakon hari da aka kai a yankin mujayada dake khan yunus

Haka zalika majiyar ta ce wasu matashi bafalasdine ya jikkata bayan da sojojin Isra’ila suka bude masa wuta, a yankin karaj dake tsakiyar khan yunus, wasu falasdinawa guda 7 kuma sun jikkata bayan da jirgin yaki Isra’ila ya kai hari kan gidaje a sansanin yan gudun hijira na shadi dake yammacin gaza bayan sanar da gargadin ficewa daga gadaje

Haka zalika sojojin Isra’ila sun harba makamai masu linzami a gabashin garin karara dake arewacin khan yunus sai dai babu wani labara na adadin wadanda suka mutu ko kuma suka jikkata a wajen,a arewacin yankin gaza kuwa wani bafalasdine yayi shahada wasu guda 3 kuma sun jikkata ciki har da yara kanana sakamakon harin da sojoji isra’ila suka kai a wuraren daban daban a hayyi rumal dake yankin gaza

Kuma wannan yana zuwa ne duk da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma a ranar 10 ga watan oktoban shekara ta 2023, isra’ila ta ci gaba da kai hare hare kullum a yankin gaza da yayi sanadiyar shahadar falasdinawa 1209 yayin da 3943 kuma suka jikkata mafiyawancinsu mata ne da yara kanana da kuma ruda gidaje masu yawa na falasdinawa

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted