EU, Ta Bukaci A Gaggauta Tsagaita Don Yi Yaran Falasdinawa Riga Kafin Polio

Shugaban kula da manufofin ketare na kungiyar Tarayyar Turai Josep Borrell ya yi kira da a gaggauta tsagaita bude wuta na kwanaki uku a Gaza

Shugaban kula da manufofin ketare na kungiyar Tarayyar Turai Josep Borrell ya yi kira da a gaggauta tsagaita bude wuta na kwanaki uku a Gaza domin ba da damar yi wa yara allurar rigakafin cutar shan inna, wanda saurin yaduwarta ke barazana ga dubban daruruwan yara a yankin Falasdinawa da aka yiwa kawanya.

Borrell yayi gargadi game da saurin yaduwar kwayar cutar mai saurin yaduwa wacce aka gano a cikin samfuran najasa da UNICEF ta tattara daga Khan Younis da Deir al Balah.

Ya ce a cikin wani sako a kan X cewa cutar, wadda za ta iya haifar da nakasu, “tana barazana ga dukan yara a Gaza, wandanda tuni suka galabaita saboda rashin abinci mai gina jiki.”

Borrell ya bukaci “a tsagaita bude wuta na kwanaki 3 nan take don ba WHO da UCICEF damar yin rigakafin ba tare da wani sharadi ba.”

Yanzu haka sama da allurar rigakafin cutar shan inna miliyan 1.2 sun isa yankin zirin Gaza, inda ake sa ran karin miliyoyin a cikin kwanaki masu zuwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments