ECOWAS Ta Amince Da Ficewar Kasashen Nijar, Mali Da Burkina Faso A Cikinta

Shugabannin kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS ko CEDEAO sun amince da ficewar kasashen Nijar da Mali da kuma Burkina Faso daga

Shugabannin kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS ko CEDEAO sun amince da ficewar kasashen Nijar da Mali da kuma Burkina Faso daga cikin kungiyar.

Hakan na nufin daga ranar 29 ga watan Janairu na shekara mai kamawa  2025 kasashen uku za su daina zama mambobin kungiyar ta ECOWAS.

Shugabannin sun dau wannan matakin ne a karshen taronsu na koli da suka yi a Abuja fadar mulkin Najeriya a ranar Lahadi.

A sanarwar bayan taron kolin da suka fitar, shugabannin kasashen na ECOWAS sun ce suna mutunta wannan matsaya da kasashen uku suka dauka ta raba gari da ECOWAS.

Amma kungiyar ta ce kwamitin rarrashin kasashen na ECOWAS wanda shugabannin kasashen Senegal da kuma Togo ke jagoranta zai ci gaba da zawarcin kasashen uku, idan sun sake shawara.

To saidai gabanin taron kasashen uku na Sahel sun ce bakin alkalami fa ya riga ya bushe game da matakin nasu na ficewa, kuma duk wasu tanade tanade na fige da fice da walwala tsakanin kasashen kungiyar ta Ecowas musamman ga al’umomin yankin yana nan daram.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments