Duniya Na Nuna Damuwa Game Da Rikicin Isra’ila Da Hizbullah

Kungiyar Tarayyar Turai ta nuna matukar damuwa game da karuwar rikicin da ke tsakanin Isra’ila da kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, kuma tana kira da

Kungiyar Tarayyar Turai ta nuna matukar damuwa game da karuwar rikicin da ke tsakanin Isra’ila da kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon, kuma tana kira da a tsagaita bude wuta cikin gaggawa, in ji babban jami’in harkokin wajen kungiyar Josep Borrell.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Borrell ya ce “Tarayyar Turai ta damu matuka game da halin da ake ciki a Labanon bayan harin da aka kai ranar Juma’a a Beirut.

Ita ma Birtaniya ta yi kira da a gaggauta tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila, da Hezbollah.

Sakataren harkokin wajen Birtaniya David Lammy ya yi kira da a tsagaita bude wuta cikin gaggawa bayan da aka samu tashin hankali tsakanin Isra’ila da kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon, yayin da karuwar tashe-tashen hankula a kan iyaka ya haifar da fargabar barkewar yaki.

Muna bukatar tsagaita bude wuta nan take daga bangarorin biyu domin mu cimma matsaya ta siyasa, ta yadda ‘yan Isra’ila da na Lebanon su koma gidajensu da rayuwa cikin kwanciyar hankali da tsaro,” in ji Lammy a jawabin da ya yi a taron shekara-shekara na jam’iyyar Labour.

Shi wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Labanon ya yi irin wannangargadin, game da “mummunan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya, a tashin hankali na tsakanin Isra’ila da Hezbollah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments