Bangarori daban-daban na duniya na ci gaba da yin tir da Allawadai da hare-haren Isra’ila kan kasar Lebanon.
A cikin bayanin da ya fitar, ofishin jakadancin kasar Irana birnin Beirut na kasar Lebanon ya yi Allawadai da hare-haren na Isra’ila a cikin kasar Lebanon, da hakan ya hada da hare-hare ta hanyar na’urorin sadarwa, da kuma harin da Isra’ila ta kai wannan Juma’a a kan tsakiyar gidajen jama’a a birnin Beirut.
Bayanin na ofishin jakadancin Iran ya ce, Isra’ila ta wuce gonad a iri a cikin wadannan ayyuka nata na ta’addanci, kuma tabbas hakan ya kara fito da aniyarta a fili na ci gaba da yin fatali da dokokin kasa da kasa da aiwatar da kisan gilla a ko’ina a cikin yankin.
Kungiyar Hamas a cikin bayanin da ta fitar ta yi Allah wadai da harin na Isra’ila, tare da bayyana cewa hakan ba zai karawa ‘yan gwagwarmaya komai ba illa kwarin gwiwa wajen ci gaba da tunkarar zaluncin Isra’ila da kuma masu mara mata baya.
Kasashen duniya da dama dad a suka hada hard a wasu na turai, duk sun fitar da bayanai daban-daban na yin tir da Allawadai da wadanann munanan ayyuka na Haramtacciyar Kasar Isra’ila a cikin kasar Lebanon, tare da bayyana hakana matsayin wani yunkuri na neman fadada yakin da take yi a Gaza zuwa wasu kasashen yankin.