Rahotonni daga haramtacciyar kasar Isra’ila sun bayyana Cewa: Duk da cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta tsakanin gwamnatin mamayar Isra’ila da ‘yan gwagwarmayar kungiyar Hizbullahi ta kasar Labanon, yahudawan sahayoniyya mazauna yankin arewacin haramtacciyar kasar Isra’ila da suka tsere daga matsugunansu da ke kusa da kan iyakar Lebanon da yankunan Falasdinu da aka mamaye sun ki komawa matsugunan nasu.
Wakilin gidan talabijin na Al-Alam da ke birnin Qudus Khidir Shaheen ya watsa rawaito cewa: Shugabannin Majalisun matsugunan yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida da suke kusa da kan iyakar kasar da Lebanon a arewacin Falastinu da aka mamaye, sun ki amincewa da komawa matsugunansu duk kuwa da cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta da ta fara aiki, kuma an samu masu gudanar da kiraye-kirayen yin zanga-zanga kan nuna adawa da shawarar Netanyahu kan amincewa da wannan yarjejeniyar.
Wasu ministocin yahudawan sahayoniyya sun yi watsi da yarjejeniyar, ciki har da Ben Gvir ministan tsaron cikin gidan Isra’ila, wanda ya yi barazanar rusa gwamnatin gamayyar haramtacciyar kasar Isra’ila idan har aka cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta bisa wannan yarjejeniya, yana mai bayyana ta a matsayin kuskuren dabaru.