Dubban dubatan mutane masu goyon bayan magajin garin Istambul a kasar Turkiya ne suka fito kan titunan birnin inda suke bukatar gwamnatin Urdugan ta sake shi.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa mutane suna ganin Ekrem Imamoglu, dan takarar shugaban kasa ne a zaben shugaban kasa mai zuwa kuma mai yuwa ya kara shugaban Urdugan a zaben, saboda yawan magoya bayansa a kasar, musamman a birnin Istambul.
Labarin ya kara da cewa Imamoglu mutum ne wanda yake da karbuwa a cikin mutanen kasar, wanda kuma ana ganin mai yuwa ya kada shugaba Urdugan a zaben shugaban kasa mai zuwa. Don haka ana ganin gwamnatin Urdugan ta sa aka kamashi, tare da zargin cin hanci da rashawa, don bata sunansa.
Gwamnatin Urdugan ta yi amfani da Jami’an tsaro don murkushe zanga-zangar masu goyon bayan magajin garin a jiya Alhamis, saboda ya ci gaba da zama mutumin da aka fi son ya ci gaba da shugabancin kasar.
Banda haka gwamnatin Urdugan ta kama Imamoglu ne bayan koma bayan da jam’iyyarsa ta gamu da shi a wani zaben da aka yi a kasar.