Dubban Falasdinawa Suna Ci Gaba Da Komawa Gidajensu Na Arewacin  Gaza

A Yau Litinin ne dai da safe dubban Falasdinawa su ka fara komawa Arewacin Lebanon bayan gushewar watanni 15 na yaki. Dubban Falasdinawan ne dai

A Yau Litinin ne dai da safe dubban Falasdinawa su ka fara komawa Arewacin Lebanon bayan gushewar watanni 15 na yaki.

Dubban Falasdinawan ne dai suke tafiya a kafa, yayin da wasu suke tafiya a cikin manyan motoci suna bi ta titin Salahuddin.

Tun da fari tashar talabijin din 12: ta HKI, ta watsa labarin cewa; sojoji sun janye daga mashigar Natsarim, da su ka kafa domin yin bincike tun ranar 27 ga watan Oktoba 2023.

Da dama daga cikin Falasdinawan sun kwana a wannan mashigar bayan da sojojin HKI su ka hana su wucewa  a jiya Lahadi.

Barin Falasdinawan su koma arewacin Gaza, yana a karkashin yarjejeniyar da aka cimmawa a tsakaninsu da Hamas,dangane da fursunonin yaki.

A jiya Lahadi kasar Katar ta sanar da cewa an cimma matsaya a tsakanin bangarorin biyu da zai bayar da damar komawar Falasdinawan zuwa gidajensu a Arewacin Gaza.

A can HKI, kafafen watsa labaru suna daukar komawar Falasdinawan zuwa gidajensu dake Arewacin Gaza a matsayin koma baya ga Isra’ila. Isra’ilan dai ta so korar Falasdinawa ne baki daya daga Arewacin Gaza da hana su komawa, domin ta gina shigen tsaro, sai dai kuma hakarta ba ta cimma tura ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments