Dubban Falasdinawa Sun Fito Kan Titunan NewYork Don Tunawa Da Ranar Musiba ko Nakba

Dubban falasdinawa ma zauna Amurka ne suka fito gagarumar zanga-zanga don tunawa da zagayowar Ranar musiba a jiya Al-Hamis a birnin NewYork. Inda suka bukaci

Dubban falasdinawa ma zauna Amurka ne suka fito gagarumar zanga-zanga don tunawa da zagayowar Ranar musiba a jiya Al-Hamis a birnin NewYork. Inda suka bukaci a kawo karshen kisan kiyashi a Gaza da gaggawa.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan shi ne musiba na shekaru 77 da suka gabata. Wato ranar da HKI to kore falasdinawa daga kasarsu bayan sun shelanta kafiwar HKI a kan kasarsu.

Falasdinawa da kawayensu daga kasashen duniya da dama su kan fito zanga-zangar tunawa da wannan ranar shekaru 77 da suka gabata a ranar 15 ga watan Mayun shekara 1948., sannan ranar Nakba ta bana tazo a dai-dai lokacinda HKI take kara kissan Falasdinawa a Gaza.

Yansanda a birnin NewYork sun tabbatar da tsaron masu zanga-zanga a duk tsawon zanga-zangar. Banda haka masu zanga zangar suna rike da tutocin falasdinawa da dama da kuma wata guda babba, wacce suka daurata a kan sanennen gada na birnin News York wanda akekira Brooklyn Bridge.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted