Hukumar tsaron DSS a Najeriya ta aike da wasika ga dandalin sada zumunta na X, wanda ake kira Twitter a da, inda a ciki ta ke bukatar ya sauke shafin dan gwagwarmaya din nan, Omoyele Sowore ko kuma ya fuskanci mataki mai tsanani .
A wasikar da hukumar ta DSS ta wallafa a shafinta na X a safiyar wannan Lahadi, ta zargi Sowore da amfani da dandalin sada zumuntar wajen caccaka da kuma yin kalaman raini ga shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu.
DSS ta yi ikirarin cewa magoya bayan Tinubu ba su ji daɗin rashin mutuncin da Sowore ya ke yi wa shugaban ba, saboda haka har sun fara zanga-zangaar rashin amincewa da hakan. Lamarin da jawo sabanin siyasa.
DSS din ta kuma gargadi X cewa za a rike shi a matsayin wanda ke taimakawa wajen haddasa husuma idan ya ki daukar mataki, tana mai jaddada cewa da mawallafin da dandalin duk su na da laifi a dokokin Najeriya.