Gwamnatin tarayya ta kammala cikakken tsarin manhajar koyarwa na makarantun bai daya da suka shafi na babbar Sakandare da kuma ilimin fasaha, wadanda aka yi da zummar samar da hanyoyin da za su bunkasa lamarin koyon karatu da irin sakamakon da za a samu.
Da take bayyana irin ci gaban da aka samu a madadin Ministan ilimi karamar Ministan, Dakta. Maruf Tunji Alausa, karamar Ministar ilimi Farfesa Suwaiba Sai’d Ahmad, ta ce sake yadda manhajar da aka yi tare da tuntubar hukumomin bincike da bunkasa ilimi(NERDC),na bai daya da kuma UBEC dake shirya Jarabawar kammala Sakandare NSSEC, da mai kula da ilimin fasaha NBTE sai kuma sauran masu ruwa da tsaki.
Kamar yadda ta bayyana,sabon tsarin ilimi ta banagaren samar da daidaito ta bangaren darussan da za’ayi da fahimatar lamarin a bayyane zai fara aiki ne a shekarar karatu ta 2025/26.
Ahmad ta bayyana cewa manhajar an tsara ta ne saboda an rage abubuwan da ta kunsa, aka kara maida hankali ga koyo domin tabbatar da cewa lamarin da ya shafi ilimi ya ci gaba da zama yana tafiya daidai da zamanin da ake ciki yanzu a fadin duniya baki daya.