DRC Ta Sa Kudi Dalar Amurka Miliyan 5 Akan Jagororin ‘Yan Tawayen M 23

Gwamnatin jamhuriyar demokradiyyar congo ta ware kudi da sun kai dalar Amurka miliyan 5 akan duk wanda ya kamo mata shugabannin  kungiyar ‘yan tawaye ta

Gwamnatin jamhuriyar demokradiyyar congo ta ware kudi da sun kai dalar Amurka miliyan 5 akan duk wanda ya kamo mata shugabannin  kungiyar ‘yan tawaye ta M 23 da su ka hada Corneelle Nangaa, Sultani Makenga da kuma Betrand Bisimwa.

Sai dai duk da kudade masu tsokar da DRC din ta sanya akan shugabannin kungiyar su uku, abin da kamar wuya,saboda ganin yadda wannan kungiyar take ci gaba da kutsawa cikin manyan birane tana shimfida ikonta a cikinsu.

A halin yanzu biranen Goma da Bukavu da suke a gabashin wannan kasa sun shiga karkashin ikon mayakan kungiyar ta M 23.

Dubban mutane ne dai su ka rasa rayukansu yayin da wasu dubun dubata kuma su ka bar gidajensu zuwa inda za su tsira da rayukansu.

Shugaban kasar ta DRC Felix Tashisekedi ya kira yi kungiyoyin kasa da kasa da su kakaba wa kasar Rwanda takunkumi saboda yadda take goyon baya da kuma taimaka wa kungiyar M23 da take ci gaba da rike da biranen Goma da Bukavu.Da akwai sojojin Rwanda 4,000 da suke taimakawa ‘yan tawayen na M 23.

Shugaban kasar ta DRC ya zargi Rwanda da wawason albarkatun karkashin kasar da ake kiyasin cewa sun kai na biliyoyin daloli.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments