Ma’aikatar harkokin wajen Denmark ta sanar da rufe ofisoshin jakadancinta da ke Mali da Burkina Faso saboda cigaba da kasancewar mulkin soji a kasashen.
Denmark ta ce a maimakon haka, za ta kara fadada alakarta da kasashen Senegal da Rwanda da Tunisia.
Wannan matakin na Denmark ya biyo kora ambasadan Sweden da aka yi daga kasar Mali bayan kasar ta Sweden ta yi barazanar daina ba Mali kayayyakin agaji saboda goyon bayan da kasar ta Mali take yi wa Rasha a yakinta da Ukraine.