Parstoday- Wakilin Iran a wasan guje-guje da tsalle-tsalle ya ki karawa da wakilin gwamnatin sahyoniyawan a gasar tsofin zakarun duniya, domin nuna goyon baya ga al’ummar Palastinu da ake zalunta.
Yanzu haka dai ana gudanar da gasar manyan wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya a birnin Gothenburg na kasar Sweden.
A rahoton Parstoday, gogaggen dan tseren kasar Iran “Masoud Bahrami” duk da cewa yana daga cikin wadanda suka yi nasara a matakin share fagen gasar tseren mita 100 na wannan gasa, da kuma kaiwa ga matakin karshe na gasar, saboda hada shi da wakilin gwamnatin yahudawan sahyoniya ta Isra’ila, yaki yin wasan domin nuna cikakken goyon bayansa al’ummar Falasdinu da yahudawa ke zalunta.
Kamar yadda Bahrami ya nuna a matakin farko na gasar tseren mita 100, ya samu babbar dama ta lashe lambar yabo a wannan gasa.
Bahrami ya samu nasarar lashe lambobin a wannain tseren mita 200 na gasar manyan wasannin motsa jiki ta duniya.
Wannan dai ba shi ne karon farko da ‘yan wasan kasar Iran suke nuna irin wannan matsaya ta jarunta a gaban ‘yan wasan gwamnatin yahudawan sahyuniya ba, kamar yadda kuma akwai ‘yan wasa daga kasashen musulmi da na larabawa da dama da suka nuna irin wannan mataki na jarunta.