Dan Takarar Jam’iyyar Adawa A Senegal Yana Gaba A Yawan Kuri’in Da Aka Irga

Bassirou Diomaye Faye dan takarar shugaban kasa daga daya daga cikin jam’iyyun hamayya a kasar yana kan gaba a yawan kuri’an da aka irga ya

Bassirou Diomaye Faye dan takarar shugaban kasa daga daya daga cikin jam’iyyun hamayya a kasar yana kan gaba a yawan kuri’an da aka irga ya zuwa yanzu da ake bada wannan labarin.

Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta bayyana cewa Bassirou Diomaye Faye dan shekara 44 kacal a duniya yana gaba da dukkan yan takara 18 da suke takara da shi a zaben na ranar Lahadi.

Labarin ya kara da cewa Amadou Ba dan takarar jam’iyyu masu mulkin kasar ya bayyana cewa mafi munin sakamakon da yake sauraro shi ne za’a sake zuwa zabe zagaye na biyu, idan har bai lashe zaben ba.

Tuni dai magoya bayan Faye sun bazu kan titunan Daka babban birnin kasar suna murnan cewa dan takaransu zai lashe zaben.

Faye dai ya shiga takarar shugabancin kasar ne a madadin jagoran yan adawar kasar Usman sonko wanda kotun tsarin mulkin kasar ta hana shi shiga takarar zaben karo na 6 a kasar.

Shugaba Maki Salla dai zai sauka daga kan kujerar shugabancin kasar bayan yayi wa’adi guda biyu a matsayin shugaban kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments