Dan Takarar Jam’iyya Mai Mulki A Kasar Ghana, Ya Amince Da Shan Kaye Ya Kuma Taya Dan Takarar Jam’iyyar Adawa Murnar Lashe Zabe

Mataimakin shugaban kasar Ghana Muhamadu Bawumia, yan amince da shan kaye a zaben shugaban kasa da nay an majalisar dokoki, wanda aka gudanar a ranar

Mataimakin shugaban kasar Ghana Muhamadu Bawumia, yan amince da shan kaye a zaben shugaban kasa da nay an majalisar dokoki, wanda aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata a duk fadin kasar. Ya kuma aike da sakon taya murna ga dantakarar Jam’iyyar adawa, kuma tsohon shugaban kasar John Hahama.

Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto Mr Bawumia ya na fadar haka a jiya Lahadi, a lokacinda yake jawabi kafin hukumar zaben kasar ta bada sanarwan sakamakon zaben.

Mahamadu wanda ya tsayawa jam’iyyarsa mai mulki wato ‘New Patriotic Party (NPP) ya ce: Sakamon zaben da Jam’iyarsa ta tara ya tabbatar da cewa, jam’iyyar adawa ta National Democratic Congress (NDC),   ta lashe zaben shugaban kasa da na majalisar dokoki gaba daya. Don haka ya mika sakon taya murna ga zabebben shugaban kasa kuma tsohon shugaban kasar John Mahama.

Mataimakin shugaban kasar ya godewa yan jam’iyyarsa da kokarin da suka yin a ganin ya lashe zaben shugaban kasa, ya kuma bukaci kasar Ghana ta zauna lafiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments