Daliban Kasar Bangaladesh Sun Kona Gidan Tsohon Shugaban Kasa

Rahotanni da suke fitowa daga kasar ta Bangaladesh sun ce, a jiya Laraba da marece ne wasu dalibai da sauran mutanen gari sun ka cinna

Rahotanni da suke fitowa daga kasar ta Bangaladesh sun ce, a jiya Laraba da marece ne wasu dalibai da sauran mutanen gari sun ka cinna wuta a cikin gidaje masu yawa, da su ka hada da na tsohon shugaban kasa Mujibur Rahman.

Abinda yake faruwa yana nuni ne da dambaruwar siyasa da kasar take ci gaba da fuskanta da kuma rashin gamsuwar da mutanen kasar nunawa akan halin da ake ciki.

Masu bin diddigin abinda yake faruwa a cikin  kasar ta Bangaladesh suna cewa, kai hari a gidan Mujibur Rahman da ake girmamawa a fadin  kasar yana nuni da zurfin matsalar da kasar take ciki.

Masu Zanga-zangar suna bayar da taken yin kira ga juyin juya hali a kasar a lokacin da suke yin kone-kone.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments