Dalibai Yan Najeriya 161 Ne Aka Hanasu Shiga Kasar Burtaniya Saboda Kasa Tsallaka Bincike Na Kan Iyaka

Dalibai yan Najeriya 1,425 ne gwamnatin kasar Burtaniya ta hanasu shiga kasar daga shekara ta 2021 zuwa shekara ta 2023 bayan sun isa kasar don

Dalibai yan Najeriya 1,425 ne gwamnatin kasar Burtaniya ta hanasu shiga kasar daga shekara ta 2021 zuwa shekara ta 2023 bayan sun isa kasar don Karin karatu saboda matsalolin da suka danganci sharuddan shige da fice.

Shafin yanar gizo na labarai ‘Afirka News’ ya bayyana cewa daga cikin wannan adadin, dalibai 161 sun sami damar shiga kasar Burtania ne ta babban shafin kasar wacce doka ta ‘yencin samun bayanai’ ta amince masu su yi hakan.

Labarin ya kara da cewa dalibai yan kasar Indiya, sune a gaba, daga cikin wadanda aka maidasu kasashen bayan sun isa kasar Burtaniya tare da kashi 45%. Sai daliban Najeriya da kashi 11.3%, sannan kasashen Ghana da Bangaldesh masu kashi 6.46% da 6.32% a jere.

Labarin ya kara da cewa wannan adadin bai hada da wadanda aka kora daga kasar ta Burtaniya saboda sabawa sharuddan zama a kasar ba, da kuma wadanda aka kora saboda dabi’u mara kyau.

Labarin ya kara da  cewa a wasu lokuta  jami’an tsaro na kan iyakar kasar sun bata visar dalibai idan sun kasa amsa tambayoyi dangane da karatunsu, ko kuma idan sun gano cewa basu iya turanci sosai ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments