Kafofin yada labaran yahudawan sahayoniyya sun tabbatar da harba makami mai linzami daga kasar Yemen, lamarin da ya tabbatar da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama zuwa da kuma tashi daga filin jirgin sama na Ben Gurion da ke Lod.
Jaridar haramtacciyar kasar Isra’ila ta Yedioth Ahronoth ta rawaito cewa: An dakatar da sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na Lod tare da jinkirin jirage masu saukar ungulu, inda aka ce sama da yahudawan sahayoniyya miliyan guda ne suka tsere zuwa maboyar karkashin kasa sakamakon makami mai linzami da aka harba daga Yemen.
A halin da ake ciki na takunkumin hana zirga-zirgar jiragen sama da Yemen ta kakaba a filin jirgin sama na Lod, kamfanonin jiragen sama na kasa da kasa suna ci gaba da soke jigilarsu zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila.
Jaridar ‘Isra’ila Hayom’ ta ‘yan sahayoniya ta bayar da rahoton cewa: Kamfanin jiragen saman Faransa Air France da na kasar Holland na Transavia suna tsawaita lokacin dakatar da zirga-zirgar jiragensu zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila har zuwa ranar 24 ga watan Mayu.