Dakarun Sojin Amurka Sun Isa Najeriya Gabanin Kaddamar Da Hari KanYan Ta’adda

Rahotanni sun bayyana cewa zangon farko na dakarun sojin Amurka da kuma jiragen yaki guda biyar sun isa Arewa maso gabashin kasar gabanin kaddamar da

Rahotanni sun bayyana cewa zangon farko na dakarun sojin Amurka da kuma jiragen yaki guda biyar sun isa Arewa maso gabashin kasar gabanin kaddamar da shirin hadin guiwa na kai hari kan kungiyoyin dake da alaka da kungiyar ISWAP mai yunkurin kafa Daular Musulunci a yammacin Afrika

Rahoton ya ci gaba da cewa jirgin yakin Amurka ya sauka a sansanin soji na mauduguri a daren ranar Alhamis yayin da da yammacin ranar juma’a kuma an ga  jiragen yaki guda 3 a wajen suna sauke kayayyakin aiki daga daya daga cikinsu.

kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana cewa kasar Amurka za ta aike da dakarun sojinta guda 200 domin bawa sojojin nageriya horo adaidai lokacin da kasar ke ci gaba da fada da rashin tsaro a yankuna daban daban a Arewa masu gabashin kasar.

wannan yana zuwa ne bayan kara fadada dangantar tsaro tsakanin Nigeriya da Amurka  bayan yajeneniyar diplomasiya da aka cimma tsakani shugaban Amurka Donald trump da kuma mahukumtan najeriya, wani kwararre kan yaki da taaddanci Brant Philip ya bayyana cewa jiragen yakin Amurka sun sauka a  barikokin sojojin saman kasar a fadin arewacin kasar a yan kwanakin nan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted