Dakarun Kungiyar Hizbullah Sun Yi Ruwan Wuta Kan Sansanin Sojojin HKI A Arewacin Kasar Falasdinu Da Aka Mamaye

Dakarun kungiyar Hizbullah na kasar Lebanon sun yi ruwan wuta a kan sojojin yahudawa yan mamaya a kan iyakar kasar da kasar Falasdinu da aka

Dakarun kungiyar Hizbullah na kasar Lebanon sun yi ruwan wuta a kan sojojin yahudawa yan mamaya a kan iyakar kasar da kasar Falasdinu da aka mamaye, daga ciki har da cibiyan sojojin yahudawan masu kissan kwamandojin kungiyar.

Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nalato majiyar kungiyar na cewa, dakarun kungiyar sun kai hare hare kan cibiyar gudanarwan ayyukan sojojin sama na HKI da ke Meron tare da amfani da makamai masu linzamu samfurin katusha. Kungiyar ta maida martani ne ga hare haren da sojojin yahudawan suka kai kan gidajen mutane a kauyukan kudancin kasar.

Banda haka dakarun kungiyar sun cilla makaman katusha da dama kan cibiyar tsaron sararin samani na sojojin HKI a arewacin kasar. Da cibiyar tsaron sama na 188 karkashin runduna ta 36 da ke Thaqnatul Alika.

Kamar yadda ta saba kungiyar Hizbullah ta bayyana cewa tana kai wadannan hare hare ne don tallafawa Falasdinawa a Gaza, da kuma maida martani ga hare haren da yahudawan suke kaiwa kan mayakan kungiyar a kudancin kasar.

A yau Asabar ma kungiyar ta yi jana’izar wasu daga cikin  shahidan ta a kudancin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments