Dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun bayyana cewa: Garuruwan da suke dauke da rumbunan makamai masu linzami na Iran kamar wani dutse ne mai aman wuta da zai iya tashi a kowane lokaci
An kaddamar da wani sabon birnin makamai masu linzami na Iran a gaban Manjo Janar Hossein Salami, babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC) da kuma Birgediya Janar Amir Ali Hajizadeh, kwamandan rundunar sojojin sama ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci “IRGC”.
Wani sabon birnin ajiyar makamai masu linzami an bayyana shi da cewa: Yana da kaso mai tsoka a shirin harin “Alkawarin Gaskiya na 2” wanda ya lalata sansanin “Nevatim” na gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a tsakiyar yankunan da aka mamaye.
A cewar hotunan da aka dauko na sansanin, ya ƙunshi makamai masu linzami na “Emad”, “Qadr” da “Qiyam”, waɗanda ake la’akari da su a matsayin tsararrun dabarun tsaro na tushe.