Mai ba da shawara ga kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Tabbas za a aiwatar da harin daukan fansa na “Alkawarin Gaskiya na 3”
Mai ba da shawara ga babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Ibrahim Jabbari ya jaddada cewa: Tabbas za a gudanar da harin daukan fansa na “Alkawarin gaskiya na 3 a daidai lokacin da ya dace, kuma daidai da karfin da ya dace, kuma harin zai rusa ci gaban gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila musamman a birnin Tel Aviv da Haifa.
A jawabin da ya gabatar a yayin atisayen fiyayyen halitta Manzon Allah {s.a.w} na dakarun sa-kai na Iran a birnin Birjan da ke gabashin kasar Iran, Birgediya Janar Jabbari ya ce: Shahidai biyu Hajj Qassem Soleimani da Sayyed Hassan Nasrallah, ta hanyar aikinsu na ilimi, sun samu damar tarbiyantar da jagorori masu jajircewa da kwarjini, wadanda dukkaninsu masu adawa ne da dabi’ar girman kai da kama karya.