Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Sun Bayyana Tsaigaita Bude Wuta A Gaza A Matsayin Nasara Ga ‘Yan Gwagwarmaya

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun bayyana cewa: Tsagaita bude wuta a Gaza babbar nasara ce a kan ‘yan sahayoniyya da ba

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun bayyana cewa: Tsagaita bude wuta a Gaza babbar nasara ce a kan ‘yan sahayoniyya da ba za a iya misalta ta ba

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun fitar da sanarwa  inda suke taya kungiyar gwagwramayar Musulunci ta Hamas da gwagwarmayar Musulunci ta Falastinu murnar nasarar da suka yi na sanya yahudawan sahayoniyya amincewa da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza, tare da la’akari da wannan tsagaita bude wuta a matsayin gagarumar nasara maras misaltuwa a kan munanan manufofin yahudawan sahayoniyya.

Kawo karshen yakin da tilastawa yahudawan sahayoniyya amincewa da tsagaita bude wuta wata babbar nasara ce a kan ‘yan sahayoniyya masu dauke da zukatan dabbobi da rashin dan Adamtaka, kuma babbar nasara ce ga al’ummar Falastinu, lamarin da ya sanya al’ummar Gaza masu karfi suka koma cikin farin ciki da kuzari da kuma juriya zuwa gidajensu. A daidai lokacin da jagoran masu zubar da jini da gwamnatinsa ta bogi za su fuskanci mummunar guguwar suka, zanga-zanga da rarrabuwar kawuna a cikin al’ummar ‘yan Sahayoniyya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments