Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun jaddada cewa: Duk wata barazana ga tsaron Iran za ta fuskanci kakkausan martani mai zafi fiye da tunani
Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun fitar da sanarwar cikan kwanaki 40 da shahadar shahidan Iran a lokacin wuce gona da iri na yahudawan sahayoniyya da Amurka, inda suka jaddada cewa: Duk wata barazana ga tsaro da yankin kasar Iran za ta fuskanci kakkausar martani da ya zarce tunanin makiya, kuma zasu kasance mafi tsanani fiye da abin da ya faru gamakiya da amsu kiran yaki a martanin alkawarin gaskiya na uku.
A cikin wata sanarwa da Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran suka fitar a cikan kwanaki arba’in da shahadar gwarazan kasa Dakarun IRGC sun jaddada cewa: Suna tare da sauran jami’an kasar a kodayaushe kuma suna shirye wajen mayar da martani mai tsauri da kakkausan mayar da martini kan duk wata barazana ko ta’addanci daga Amurka ko ‘yan sahayoniyya ko kuma kawayensu.