Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Sun Bayyana Sabon Salon Mayar Da Martani Kan Isra’ila

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun yi bayani kan sabon salon mayar da martani kan Isra’ila a harin ‘Alkawarin Gaskiya na 3″

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun yi bayani kan sabon salon mayar da martani kan Isra’ila a harin ‘Alkawarin Gaskiya na 3″

Ma’aikatar hulda da jama’a ta dakarun kare juyin juya halin Musulunci ta Iran a cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin jiya Asabar ta sanar da cewa: Dakarun tsaron sararin samaniyar IRGC sun kaddamar da wani sabon farmakin hadin gwiwa na “Alkawarin Gaskiya na 3” ta hanyar amfani da makamai masu linzami da jirage masu saukar ungulu a matsayin mayar da martani ga sabon farmakin da yahudawan sahayoniyya suka yi kan yankunan Iran.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar hulda da jama’a ta IRGC ta fitar ta bayyana cewa: Dakarun tsaron sararin samaniyar IRGC sun kaddamar da wani sabon salon farmakin hadin gwiwa na “Alkawarin Gaskiya na 3” kan yankunan haramtaciyar kasar Isra’ila da muhimman cibiyoyinta ta hanyar amfani da makamai masu linzami da jirage marasa matuka don mayar da martani ga sabon harin wuce gona da iri da yahudawan sahayoniyya suka yi kan yankunan kasar Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments