Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Sun Bayyana Cewa: Makamai Masu Linzaminsu Zasu Kai Duk Inda Makiya Suke

Babban kwamnandan dakarun kare juyin juya halin Musuluncin na Iran ya jaddada cewa: Makamai masu linzamin Iran za su iya kai hari kan kowane makiyi

Babban kwamnandan dakarun kare juyin juya halin Musuluncin na Iran ya jaddada cewa: Makamai masu linzamin Iran za su iya kai hari kan kowane makiyi

Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Manjo Janar Husaini Salami ya tabbatar da cewa: Makamai masu linzami na Iran suna da karfin kai hari kan duk wani wuri da ke da alaka da makiya a yankin da kuma fatattakar makamai masu linzami, yana mai jaddada cewa; sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci suna da karfin kalubalantar makiya a kowane lokaci.

Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musuluncin ya gabatar da jawabi ne a wajen bikin “Malik Ashtar” karo na 14 a safiyar yau Litinin, inda ya ce an kafa dakarun kare juyin juya halin Musulunci ne a matsayin wata mu’ujiza ta ilimi da ta samu kwarin gwiwar abubuwan da suka faru a farkon nasarar juyin juya halin Musulunci na farko, albarkacin wannan rana bisa hangen nesa na marigayi Imam Khumaini {yardan Allah ta tabata a gare shi}.

Ya kara da cewa mayakan da ke kan iyaka suna wakiltar ginshikan tsaro da martabar kasar. Yana mai bayyana cewa: Idan kasar Iran ta samu jin dadin zaman lafiya a cikin tekun wuta, hakan na faruwa ne sakamakon sadaukarwar da wadannan mayaka suka yi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments