Dakaru na musamman daga rundunar kare juyin juya halin musulunci (IRGC) a nan Iran da kuma sojojin kasar Azairbaijan sun fara atisayen hadin giwa a tsakaninsu a jiya Lahadi.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar IRGC na cewa atisayen zai dauki kwanaki 4 cur ana gudanarwa. Sannan manufar sa itace ce karfafa harkokin tsaro a kan iyakar kasashen biyu, musamman a bangaren yaki da yan ta’adda da kuma musayar dabarbarun yaki.
Kafin haka dai kasashen biyu, musulmi sun kulla yarjeniyar tsaro a tsakaninsu, wanda ya basu damar aiki tare da kuma bunkasa harkokin tsaro a tsakanin kasashen biyu.
Atisayen wanda aka sanyawa suna ‘Gamayyar Aras’ zai taimakawa kasashen biyu sabawa da yanayin kan iyakar kasashen biyu
Wannan dai shi ne atisayen soje mafi girma a tsakanin kasashen biyu sannan kuma ana gudanar da shi ne a lardin Ardabil na kasar Iran wanda kuma yake kan iyakar kasashen biyu.