Dakarun Kai Daukin Gaggawa Na Sudan Sun kashe ‘Yan Hijira Da Dama A Yankin Tekun Maliya

A wani hari da jirgin sama maras matuki da dakarun kai daukin gaggawa su ka kai akan sansanin ‘yan hijira a Jahar ” Nahrun-Nil” a

A wani hari da jirgin sama maras matuki da dakarun kai daukin gaggawa su ka kai akan sansanin ‘yan hijira a Jahar ” Nahrun-Nil” a Arewacin Sudan sun kashe mutane da dama da kuma jikkata wasu, haka nan kuma sun yi sanadiyyar yanke wutar lantarki a yankin.

Kafar watsa labaru ta “al-muhakkak” ta ce; Dakarun kai daukin gaggawar sun kai hari da jirgin sama maras matuki akan sansanin ‘yan hijira da ya yi sanadiyyar mutuwar da dama daga cikinsu da kuma yanke wutar lantarki a garin Atbarah, a jihar “Nahrun-Nil” ta arewa.

Hukumar dake samar da wutar lantarki ta Sudan ta tabbatar da yankewar samar da wuta a wannan yankin saboda harin da mayakan na rundunar daukin gaggawa su ka kai.

Kamfanin samar da wutar lantarki na Sudan ya tabbatar da cewa, ‘yan kwana-kwana suna matukar kokarinsu domin kashe gobarar da ta tashi.

Kwamitin tsaro a jihar ta “Nahrul-Nail” ya bayyana wannan irin harin da cewa; Yankan baya ne, kuma ana kai shi ne akan fararen hula da kuma muhimman cibiyoyin dake cikin Jahar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments