Dakarun Juyin Juya Halin Musulunci Sun Kera Sabon Jirgin Sama Mara Matuki Ciki

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun kera wani jirgi maras matuki ciki mafi girman da suka Sanya masa suna “Gaza” A jiya

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun kera wani jirgi maras matuki ciki mafi girman da suka Sanya masa suna “Gaza”

A jiya Lahadi, a gefen atisayen soji mai taken “Manzon Allah Mai Girma na 19” da aka gudanar da gwajin makamansu, sun samu nasarar gwajin sabon jirgin sama maras matuki ciki mai suna “Gaza” wanda ake daukansa a matsayi mafi girman jirgin saman maras matuki ciki da zai iya yin luguden wuta mafi girma da tsanani, jirgin yana cin dogon zango kuma shi ne mafi girma da Iran ta kera wajen kai farmakin da zai jefa bama-bamai 8 akan wurare 8 a kasa.

Jirgin Gaza maras matuki (wanda ake kira Shahed 149) shi ne jirgi mara matuki mafi tsayi da Iran ta kera kuma an bayyana shi a shekara ta 2021. Wannan jirgi mara matuki mai nauyi da ya kai tsawon mita 21, kuma yana iya shawagi har tsawon sa’o’i 35. kuma rufin jirgin ya kai kilomita 10/5, gudunsa ya kai km 35 a cikin sa’a guda, sannan yana iya daukar bama-bamai da ya kai nauyin kilogiram 500, kuma karfin tafiyarsa ya fi na Shahed 129 maras nauyi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments