Search
Close this search box.

Dakarun Izzuddeen Al-Qassam Sun Kai Harin Kan Birnin Tel-Aviv Domin Daukan Fansa

Dakarun Izzuddeen Al-Qassam sun sanar da harin kan birnin Tel Aviv na haramtacciyar kasar Isra’ila da makamai masu linzami Dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar

Dakarun Izzuddeen Al-Qassam sun sanar da harin kan birnin Tel Aviv na haramtacciyar kasar Isra’ila da makamai masu linzami

Dakarun Izzuddeen Al-Qassam bangaren sojin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas sun sanar da cewa: Sun kai hare-haren bama-bamai kan birnin Tel Aviv da makamai masu linzami samfurin M90 guda biyu. A cikin wata sanarwa da dakarun suka fitar sun bayyana cewa, mayakansu mujahidai sun yi luguden makamai masu linzami guda biyu kirar M90 kan birnin Tel Aviv da kewayensa, domin mayar da martani ga kisan kiyashin da yahudawan sahayoniyya suka yi wa fararen hula da kuma ‘yan gudun hijira da kuma jama’ar gari a yankunan Falasdinawa.

Sojojin gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun sanar da harba makamai masu linzami guda biyu daga Gaza zuwa birnin Tel Aviv, kuma ba naurorin zamani sun gano zuwan makaman kan birnin ba, ballantana a hura kararrawar gargadi ba. Sannan a yammacin jiya an ji karar fashe-fashen wasu abubuwa a birnin na Tel Aviv.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments