Ci Gaban Tsaro Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Yana Sanya Makiya Iran Takaici

Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran ya bayyana cewa; Abubuwan da suka nuna irin girman dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun sanya makiya takaici

Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran ya bayyana cewa; Abubuwan da suka nuna irin girman dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun sanya makiya takaici

Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Mohammad Baqiri ya jaddada cewa bayyanar irin girman da dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran suke da shi ya sanya makiya takaici.

Hakan ya zo ne a daidai lokacin da Manjo Janar Baqiri ya aike da sakon murna ga kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci, Manjo Janar Hossein Salami, a yau Asabar, dangane da bukukuwan watan Sha’aban, ciki har da zagayowar ranar haihuwar Imam Husaini (a.s), wanda ya zo daidai da ranar dakarun kare juyin juya halin Musulunci.

Yana mai jaddada cewa; Yana da imanin cewa dakarun kare juyin juya halin Musulunci suna bayyana ne ga kowane dan kasar Iran a cikin wani yanayi mai girma a fagen gwagwarmayar Musulunci a wannan yanki, kuma hakan yana sanya al’ummar musulmi alfahari.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments